Isa ga babban shafi
Amurka

Guguwar Irma ta yi gagarumar barna a Florida

Kakkarfar guguwar Irma ta ratsa cikin tsakiyar Florida, tare da lalata wutar lantarkin ankunan da ta keta, baya ga yaye rufin gidaje da kuma mamakon ruwan saman da ya hadda ambaliya a titunan birnin jihar, Miami.

Yankin Brickell da ambaliyar ruwa ta mamaye bayan ratsawar guguwar Irma ta cikin birnin Miami, a jihar Florida.
Yankin Brickell da ambaliyar ruwa ta mamaye bayan ratsawar guguwar Irma ta cikin birnin Miami, a jihar Florida. REUTERS/Stephen Yang
Talla

Tuni dai kakkarfan ruwan saman da guguwar ke dauke da shi, ya lakume hanyoyin mota, da kuma barin miliyoyin mutane ba tare da wutar lantarki ba a Jihar ta Florida bayan ta’adin da ta yi a yankin Caribbean.

Mutane sama da miliyan 6 aka baiwa umurnin barin gidajen su domin kaucewa guguwar wadda ke da matukar hadari lokacin da ta dumfari Jihar a jiya Lahadi.

Guguwar mai tafiyar kilomita 169 cikin sa’a guda ta hallaka mutane 3 a Florida, yayin da mutane sama da miliyan 3 suka rasa wutar lantarki.

a rahotanni sun ce daruruwan mutane sun ki ficewa daga gidajen su duk da gargadin da akayi ta musu, yayinda guguwar ta lalata kanana jiragen ruwa, ta kada bishiyoyin kwakwa da turakun lantarki da kuma kwashe rufin gidaje.

Sa’oi bayan Florida, guguwar ta isa Naples inda ta raba mutane sama da miliyan biyu da wutar lantarki yayin da ruwan sama ya mamaye titunan birnin.

Shugaba Donald Trump wanda yace nan bada daewa ba zai ziyarci Florida ya amince da tallafin gaggawa ga mutanen Jihar, inda yake cewa yanzu abinda suka mayar da hankali akai shine kare rayukan mutane maimakon kudin da za’a kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.