Macron zai jagoranci taro kan matsalar kawarar baki zuwa Turai
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai jagoranci wani taro ranar litinin a Paris, wanda zai kunshi shugabanin kasashen Jamus, Italia, Spain da kuma wasu shugabannin Afirka kan yadda za’a shawo matsalar bakin da ke kwarara nahiyar Turai.
Wallafawa ranar:
Fadar Elysees, ta sanar da cewar daga cikin shugabannin da aka gayyata daga Afirka sun hada da na Chadi Idris Deby, da shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou da kuma na Libya Fayez Al-Sarraj.
Taron zai jaddada goyan bayan da kungiyar kasashen Turai ke da shi kan ga kasashen Chadi da Nijar da Libya wajen dakile matsalar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu