Isa ga babban shafi
Libya-EU

EU ta zartar da matakin kayyade sayar da jiragen ruwa ga Libya

Ministocin kasashen kungiyar tarayyar turai EU, sun amince da daukar matakin kayyade saida kana-nan jiragen ruwa, da ma wasu nau’o’in manyan jiragen, ga kasar Libya, don rage yawan bakin haure da ke kwarara zuwa turan.

Wasu bakin haure da ke kokarin ketara tekun Meditarranean zuwa nahiyar Turai.
Wasu bakin haure da ke kokarin ketara tekun Meditarranean zuwa nahiyar Turai. Reuters
Talla

Karkashin dokar wadda ta fara aiki daga jiya, za’a rika saida jiragen ruwan ne ga halatattun ‘yan kasuwar kasar ta Libya kawai, musamman wadanda suke sana’ar kamun kifi.

To sai dai majalisar ministocin bata fayyace irin matakan da zata dauka ba don ganin cewa dokar ta yi tasiri yadda ya kamata.

A lokacin da sashin Hausa na RFI ya tuntube shi, domin jin ko matakin zai yi tasiri, Farfesa Dan Datti Abdulkadir, tsohon jakadan Najeriya a kasar ta Libya, ya ce abu ne mawuyaci, idan aka yi la’akari da cewa akwai turawan da ake hada baki da su a boye, don yin safarar bakin hauren.

A cewar farfesa Dan Datti, tilas a fara magance matsalar idan har ana son magance kwarar bakin hauren daga Afrika zuwa Turai, daga nan kuma sauran matakan da za’a dauka zasu rika yin tasiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.