Isa ga babban shafi
Turai

EU ta goyi bayan saukakawa Italiya kan bakin haure

Shugabannin kungiyar tarayyar turai EU, sun goyi bayan bukatar kasar Italiya, ta neman sauran kasashen turai, su rika karbar bakin hauren da aka ceto daga tekun Medetarranian.

Wasu daga cikin dubban 'yan gudun bakin hauren da aka ceto daga cikin tekun Mediterranean.
Wasu daga cikin dubban 'yan gudun bakin hauren da aka ceto daga cikin tekun Mediterranean. REUTERS/Stefano Rellandini
Talla

Matakin ya zo ne, bayanda aka ceto akalla bakin haure dubu 10, daga tekun, a cikin kwanaki uku da suka gabata kawai.

Wata kididdiga ta hukumomin Italiya suka fitar ta nuna cewa daga farkon shekara ta 2017 da muke ciki zuwa yanzu, kasar ta karbi bakin haure da yan gudun hijira sama da dubu 82.

Hakan ya tabbatar da cewa Italiya ke a matsayin babbar hanya ko mashiga zuwa nahiyar turai ga dubban bakin haure da ‘yan gudun hijirar da ke fafutukar ketarawa zuwa nahiyar. Hakan kuma yayi matukar tasiri a siyasar kasar ta Italiya.

A makon da ya gabata, sai da jam’iyya mai mulki a kasar ta sha kashi a zaben kananan hukumomin da ya gudana, bayanda masu kada kuri’a suka gwammacewa zabar jam’iyyar adawa mai kishin kasa da ta sha alwashin rage yawan bakin hauren da kasar ke karba.

Tuni dai kungiyar tarayyar turai ta mince da kara yawan kudaden tallafin da take bai wa Italiya don daukar dawainiyar Karin bakin hauren da ke cigaba da tudada zuwa kasar a taron da ta yi a Brussels, sai dai har yanzu shugabannin na EU basu bayyana kasashen da zasu taimaka ba, koda yake sun bayyana gabar ruwan Barcelona dake Spain da Marsielle a Faransa a matsayin mafi cancanta a game da fara ragewa kasar Italiyan nauyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.