Isa ga babban shafi
Faransa

Macron da Putin sun gana a Faransa

A karon farko tun bayan darewarsa kan karagar mulki, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da takwaransa na Rasha Vladmir Putin duk da sabanin ra’ayoyin da suke da shi kan rikicin Ukraine da Syria.

Shugaban Faransa  Emmanuel Macron da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a fadar Versailles
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a fadar Versailles REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugaba Macron ya karbi bakwancin Putin ne a kasaitacciyar fadar Versailles da ke wajen birnin Paris, in da suka sha hannu sama-sama da juna.

Ana kallon wannan ganawar a matsayin zakarar gwajin dafi ga kwarewar Macron a huldar diflomasiya bayan taron kasashen duniya masu karfin tattalin arziki na G7 da ya halarta a makon jiya a Italiya da kuma na kungiyar tsaro ta NATO da ya halarta a Brussels.

Shugaba Macron ya ce, tattaunawa da Rasha na da matukar muhimmanci saboda akwai wasu batutuwan da suka shafi kasashen waje da ke bukatar zaman keke da keke don samar da masalaha a kansu.

Jakadan Rasha a Faransa, Alexander Orlov ya bayyana fatarsa ta ganin cewa, wannan ganawa ta warware tsamin danganta da aka samu tsakanin Putin da tsohon shugaban Faransa, Francois Hollande.

A lokacin yakin neman zabensa dai , Mr. Macron ya yi amfani da zafafan kamalai wajen caccakar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.