Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta zargi Rasha da yin kutse

Gwamnatin Faransa ta zargi Rasha da kokarin yin kutse domin dagula yakin neman zaben wasu ‘yan takarar shugaban kasa, kamar yadda ta faru da Amurka.

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande AFP
Talla

Shugaba Francois Hollande ya bukaci daukar matakan hana yi wa Faransa kutse a Intanet kafin lokacin gudanar da zaben shugaban kasa musamman Rasha da Amurka ta zarga ta taimakawa Donald Trump ta hanyar kutse.

Tuni dai daya daga cikin ‘Yan takarar shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fara zargin Rasha da yin kutse a shafin yakin neman zaben shi na Intanet.

Duk da cewa Shugaba Hollande ba zai nemi wa’adin shugabanci na biyu, amma ya bukaci hukumomin tsaron Faransa su sa ido tare da daukar matakan kariya daga kutse da za a iya yi wa shafukan yakin neman zaben ‘yan takarar a intanet.

A ranar 23 ga Afrilu za a gudanar da zagayen farko na zaben Faransa kuma Mista Hollande ya bayyana fargaba ne domin kaucewa zargin kutse kamar yadda ta faru da Amurka.

Ministan harakokin waje Jean-Marc Ayrault ya ce ba za su amince da Rasha ko wata kasa ta tsoma baki ga sha’anin zaben Faransa ba.

Batun dai murabus din mai ba Donald Trump shawara kan sha’anin tsaro ya kara dada tabbatar da zargin da Amurka ke yi wa Rasha na yin katsalandan ga sha’anin zabenta ta hanyar yin kutse a shafin jam’iyyar Democrat domin dagula takarar Hillary Clinton.

Gwamnatin Hollande kuma yanzu ta fara zargin Rasha da kokarin taimakawa ‘yan takarar jam’iyyun adawa masu ra’ayinta Francois Fillon da ‘yar kishin kasa Marine Le Pen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.