Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya yi bankwana da Ministocinsa

A yau Laraba Shugaban Faransa Francios Hollande mai barin gado ya jagoranci taron ministocinsa karo na karshe a matsayin shugaban kasa, yayin da a yau kuma ya gabatar da jawabi na karshe a matsayin shugaban kasa, a wani taron da suka hadu da Emmanuel Macron mai jiran gado na tuna kawo karshen bautar da bayi.

Shugaban Faransa mai barin gado François Hollande da Emmanuel Macron mai jiran gado
Shugaban Faransa mai barin gado François Hollande da Emmanuel Macron mai jiran gado REUTERS/Eric Feferberg/Pool
Talla

Yau Laraba ana ganin rana ce mai matukar muhimmaci ga Shugaba Hollande mai barin gado inda ta kasance ranar karshe da shugaban ya jagoranci lamurran tafiyar da kasa a matsayinsa na shugaban Faransa

Hollande ya jagoranci taron ministocinsa 17 na karshe a yau Laraba taron da ya kunshi sakatarorin gwamnati 20.

Sannan a yau Hollande tare da Emmenuel Macron sun sake haduwa a taron tuna kawo karshen bautar da bayi a Jardin du Luxembourg a Paris inda Hollande ya gabatar da jawabin karshe a matsayinsa na shugaba.

Wannan ne karo na biyu da Hollande suka hadu da Emmanuel Macron bayan sun hadu a ranar 8 ga Mayu kwana guda da zaben Macron a matsayin shugaban kasa.

A haduwarsu a yau Macron ya fi sakin jiki da Hollande inda aka nuna yana murmushi da raha tare da shugaban da zai karbi mulki a hannunsa a ranar Lahadi.

Bayan kammala taron ministocin, Hollande ya rako ministocinsa zuwa kofar Elysee, inda yan jarida suka yi cincinrindo suna jiran fitowar shugaban mai barin gado.

Macron dai tsohon minista ne a gwamnatin Hollande, kafin ya fice, kuma cikin shekara guda ya kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa da ya ba shi nasara a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.