Nathalie Arthaud ‘Yar takarar Zaben Faransa na 2017
Nathalie Arthaud mai gwagwarmayar kare hakkin ‘yan kwadago, na daya daga cikin ‘yan takara 11 da za su kara da juna a zagayen farko na zaben shugabancin Faransa na 2017 da za a gudanar a ranar 23 ga wannan wata na Afrilu.
Wallafawa ranar:
Tarihin Nathalie Arthaud
An haifi Nathalie Arthaud a 1970 a jihar Drôme da ke kudu maso gabashin kasar Faransa, tun tana ‘yar shekaru 18 a duniya ta tsunduma gwagwarmayar kungiyoyin kwadago.
Ta yi karatunta ne a fannin shi’anin tattalin ariziki da dangoginsa, kafin ta yi aikin koyarwa a ungunannin marasa galihu da ke birnin Lyon.
Tun a 2002, Nathalie Arthaud ta ke tsayawa takara a zabubbukan majalisun kananan hukumomi, majalisar dokoki, manyan yankunan Faransa da na kasashen turai.
Ta zama ‘Yar majalisar karamar hukumar Vaulx-en-Velin da ke jihar Lyon kafin ta zama mai magana da yawun Arlette Laguiller matar da ta taba tsayawa takarar nemen shugabancin Faransa a 2007 a yayin da a 2008 ta zama kakakin ‘yan gwagwarmayar kungiyoyin kwadagon kasar.
A 2012 ta taba tsayawa takarar neman zama ‘yar majalisar dokoki inda ta sha kaye a mazabarta ta da’ira ta 6 da ke unguwar Seine-Saint-Denis a birnin Paris.
Wannan duk bai sanyaya guiwar wannan gwarzuwar ‘yar siyasa ba, inda a 2015 ta sake yin takara a zaben yankunan Faransa da suka hada da na Ile de France ba tare da samun nasara ba.
A ranar 12 ga Maris na 2016 ne, gungun masu gwagwarmayar neman kare hakkin ‘yan kwadago ya tabbatar da ita a matsayin ‘yar takarar da za ta wakilce su a zaben shugabancin kasar na 2017.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu