Isa ga babban shafi
Faransa

Le Pen na samun tagomashi a Kuri’ar jin ra’ayi

Shugabar Jam’iyyar Front Nationale na masu Kishin kasa, Marine Le Pen, ta samu tazara sama da abokan takaranta Emmanuel Macron da Francois Fillon a kuri’ar jin ra’ayi.

Marine Le Pen na samun tagomashi a kuri'ar jin ra'ayi
Marine Le Pen na samun tagomashi a kuri'ar jin ra'ayi Reuters/Robert Pratta
Talla

Sai dai akwai yiwuwar Le Pen, ta yi rashin nasara a zageye na biyu a cewar kuri'ar.

Kuri’ar Jin ra’ayin da aka gudanar kan ‘yan takaran ya bayyana Le Pen a matsayin wacce ta doke abokan takararta 4 tare da nasara a zagayen farko na zaben da za a gudanar 23 ga watan Afrilu mai zuwa, kuma ta samu kashi 27 cikin 100 na fafatwan a zagaye na gaba da Macron ko Fillon.

Kuri’ar ta ci gaba da bayyana cewa idan ta fafata da Macron za ta samu kashi 42 kasa da shi da zai samu kashi 58, a karawarsu da Fillon kuma zata samu kashi 44 inda shi kuma zai samu kashi 56 cikin 100.

Le pen dai na da muradan janye Faransa daga EU, ta hanyar shirya zaben raba gardama, da kuma sanya haraji masu yawa kan abubuwan da ake shigowa dasu kasar da baki da ke aiki a kasar.

Makonni 9 saura aje ga rumfunar zabe, har yanzu ba za a iya tantace tsakanin Macron da Fillon wanene zai fafata da Le Pen a zagayen karshe ba.

Sakamakon kafada da kafada da suke ci gaba da yi a kuri’ar jin ra’ayin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.