Isa ga babban shafi
Faransa

An yi wa Fillon da matarsa tambayoyi a Faransa

Masu bincike a Faransa sun yi wa dan takarar shugabancin kasar Francois Fillon tambayoyi kan biyan matarsa Euro dubu 500 a kowanne wata daga asusun gwamnati ba tare da yin wani aiki ba.

Francois Fillon da matarsa Pénélope Fillon a birnin Paris na Faransa
Francois Fillon da matarsa Pénélope Fillon a birnin Paris na Faransa REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

An yi wa Fillon da matarsa Penelope tambayoyi ne daban daban dangane da wannan zargi da ake ganin zai rage wa Fillon kima a idanun masu kada kuri’u a zaben kasar mai zuwa.

Kimanin mutane dubu 208 ne suka sanya hannu kan wata takarda a shafin intanet, wadda ta bukaci dawo da kudaden na talakawa.

Fillon ya hakikance cewa, mai dakinsa ta gudanar da aikin cancantar karbar Euro dubu 500, yayin da ya zargi wasu da yada kamfen don bata masa suna.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewar, yanzu haka Marine Le Pen mai kyamar baki ke sahun gaba wajen lashe zaben da za a gudanar a watan Mayu mai zuwa, sai kuma Fillon da Emmanuel Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.