Isa ga babban shafi
Faransa

Ana neman bata min suna- Fillon

Dan takarar Shugabancin Faransa a Jam’iyyar Republican Francois Fillon ya lashi takobin wanke kansa tare da gabatar da shaidu kan zargin da ake wa matarsa na karban albashin kudi sama da yuro dubu 500 a aikin bogi.

François Fillon, da matarsa Penelope
François Fillon, da matarsa Penelope REUTERS/Charles Platiau
Talla

Dan takarar ya ce babu shaka wannan badakala ce aka shirya ta yarfen siyasa domin bata ma shi suna da takararsa.

Fillon wanda kuri’an jin ra’ayi ke nuna akwai yiwuwar ya samu nasara a zaben shugaban kasar da za a gudanar cikin watan Mayu, na fuskantar matsin lamba da bincike kan biyan matarsa kudi a matsayin albashi daga majalisa ba tare da gudanar da wani aiki ba.

Zargin da tuni ya soma haifar da cikas ga yakin neman zaben Francois Fillon, ya tilastwa lauyansa Antonin Levy ganawa da masu bincike tare da ba su takardu da zai wanke fillon.

A zantawarsa da manema labarai kan zargin, Fillon ya ce a kodayaushe matarsa na ma sa aiki.

Jaridar Canard Enchaine ce ta bankado labarin wanda ya nuna cewar matar Fillon, Penelope ta karbi yuro sama da 500,000 a wata a matsayin albashi tsakanin 2012 zuwa 2013, a lokacin da na mijinta na majalisa.

Tun kafin a je ga zaben kasar, Kuri’un jin ra’ayi na bayyana cewa Fillon zai fafata da Maria Le Pen ta jam’iyyar NF ‘Yan kishin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.