Isa ga babban shafi
EU-Birtaniya

Kasashen Turai bakwai na taro dangane da batun ficewar Birtaniya daga Kungiyar Turai

Shugabanni bakwai na kasashen kudancin Turai na taro yau Asabar a Lisbon don tsaida matsaya daya gameda ficewar kasar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai, da kuma yadda za su yi muamulla da sabuwar Gwamnatin Amurka ta Donald Trump.

Fira Ministan Portugal Antonio Costa
Fira Ministan Portugal Antonio Costa REUTERS/Rafael Marchante
Talla

Taron shine irinsa na biyu cikin watanni hudu da suka gabata, inda ake sa ran su duba batun ciyarda kasashen gaba da lamarin bakin haure.

Fira Minista Antonio Costa na kasar Portugal mai masaukin baki ya nuna cewa taron nasu nada muhimmanci don duba irin sauye-sauyen da suka dace ayi a Kungiyar Tarayyar Turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.