Isa ga babban shafi
Birtaniya

Jakadan Birtaniya a Turai ya yi murabus

Jakadan Birtaniya a kungiyar kasashen Turai Sir Ivan Rogers ya yi murabus daga wannan mukamin wanda tsohon Firaministan kasar David Cameron ya nada shi akai a shekarar 2013, kuma hakan na zuwa ne a yayin da ake zaton zai taka muhimmiyar rawa a tattaunawar ficewar kasar baki daya daga kungiyar tarayyar Turai. 

Sir Ivan Rogers mai murabus
Sir Ivan Rogers mai murabus 路透社/Francois Lenoir
Talla

Murabus din Rogers na zuwa ne a dai dai lokacin da ya rage watanni 9 ya sauka daga kujerarsa, abin da ya kara dakula shirye shiryen kasar na ficewa baki daya daga Turai.

Gwmnatin Birtaniya ta bayyana cewa za a nada wani sabon jakada da zai maye gurbin Rogers gabanin zaman tattaunawar ficewar kasar da za a yi nan da watan Maris mai zuwa.

A cikin watan jiya ne, Mr. Rogers ya sha caccaka daga ministocin Birtaniya bayan ya ce, da yiwuwar a shafe tsawon shekaru 10 kafin kasar ta kammala cimma yarjejeniyar cinikayya da kungiyar tarayyar Turai.

Ministocin dai na ganin cewa, za a iya cimma wannan yarjejeniya a cikin shekaru biyu sabanin 10 da Rogers ya fadi.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya rawaito jakadun kasashen Turai na cewa, murabus din Rogers bai zo wa da wadanda ke aiki da shi mamaki ba, yayin da suka bayyana shi a matsayin kwararre da bai gamsu da matsayin Birtaniya kan wannan lamari ba.

A cikin watan Yunin bara ne , kashi 52 cikin 100 na al’ummar Birtaniya suka zabi ficewar kasar daga Turai a kuri’ar raba gardamar da suka kada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.