Alexander Van der Bellen ya lashe zaben Austriya
Dan takarar jam’iyyar masu fafutukar kare muhalli Alexander Van der Bellen ya yi nasara akan Norbert Hofer wanda da farko aka yi hasashen cewa shi zai lashe zaben shugabancin kasar.
Wallafawa ranar:
An tabbatar da nasarar Alexander Van der Bellen bayan ya kayar da dan kishin kasa Norbert Hofer mai ra'ayin rikau.
Alexander ya samu nasara da kusan kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada a jiya Lahadi, sabon shugaban kasar ya kasance mai goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai yayin da a daya bangaren Hofer ya bayyana kansa a matsayin wanda ke adawa da bakin haure
Mr Van der Bellen ya yaba da sakamakon zaben, a jawabinsa na farko Van Der y ace launin tutar kasar ta Austria alama ce ta chanji da kyakyawar fata ga kasar da ma kasashen Tarrayar Turai
Tuni dai Mista Hoffer ya amsa shan kaye tare da meka sakon taya murna ga Alexander Van der Bellen
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande na daga cikin shugabanin kasashen duniya ta suka aika sakon taya murna ga sabon shugaban kasar ta Austria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu