An rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a Colombia
Gwamnatin Colombia da ‘yan Tawayen kasar, sun rattaba hannu akan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a wani biki da akayi a Bogota, duk da adawar da hakan da wasu ‘yan kasar keyi.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Juan Manuel Santos da shugaban ‘yan tawaye Rodrigo Timochenko Londono ne suka sa hannu a gaban daruruwan ‘yan kasar, da wani alkalami da aka kera daga harsashin da akayi amfani da shi a yakin da shafe tswon lokaci ana fafatashi a kasar.
Shugaba Santos ya shaidawa taron cewa, kowa ya san barnar da yakin da aka kwashe dogon lokaci ana yi ya haifar, saboda haka ya zama wajibi a rungumi zaman lafiya.
Ana saran gabatarwa Majalisar kasar sabuwar yarjejeniyar, domin amincewa da ita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu