Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya sha kaye a zaben fidda gwani

Yunkurin tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy na sake takarar shugabancin kasar a zaben shekara mai zuwa ya samu koma baya sakamakon shan kashin da ya yi a zaben fidda gwanin da aka gudanar jiya.

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya sha kaye a zaben fidda gwani.
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya sha kaye a zaben fidda gwani. GEORGES GOBET / AFP
Talla

Sarkozy ya sha kaye daga hannun tsofin Firaministan kasar guda biyu Francois Fillon da Alain Juppe wadanda zasu fafata a zagaye na biyu dan samun wanda zai tsayawa Jam’iyyar su takarar.

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya zo na uku ne a zaben fidda gwanin da kashi 21 yayin da tsohon Firaministan sa Francois Fillon ya zo na farko da kashi 44 sai kuma  Alain Juppe da ya zo na biyu da kashi 28 na kuri’un da aka kada.

Sarkozy ya bayyana goyan bayan sa ga takarar Francois Fillon, kuma nan take ya bayyana cewar zai janye daga harkokin siyasa.

Tsohon shugaban ya shaidawa magoya bayan sa cewar yayi iya bakin kokarin sa amma kuma hakan bai sa ya janyo ra’ayin maus zaben ba.

Sarkozy yace yana girmama Alain Juppe amma kuma manufofin sa sun fi kama da na Francois Fillon saboda haka shi zai goyawa baya.

A karshen wannan mako ne za’a gudanar da zaben zagaye na biyu tsakanin Francois Fillon da Alain Juppe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.