Faransa na shirin tsawaita wa’adin dokar ta baci
Firaiyi ministan Faransa Manuel Valls ya ce akwai yiwuwar kara tsawaita wa’adin dokar ta bacci da aka sanya a kasar bayan hare-haren ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dari daya da talatin a bara.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mista Valls ya ce akwai bukatar ci gaba da aiki da dokar ganin Faransa na shirin gudanar da babban zaben shugaban kasa al’amarin dake bukatar tsaro don kare lafiyar al’umma.
A ranar sha uku ga watan Nuwambar shekarar 2015 aka kai hare-haren ta’addancin da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 130 a Bataclan da kuma wasu filayen wasanni da ke birnin Paris.
Ana dai ci gaba da taron bukukuwan cika shekara guda da kai hare-haren birnin Paris da ya matukar girgiza al’ummar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu