Isa ga babban shafi
Italiya

An ceto ‘yan ci-rani 300 a tekun Bahrum

Masu Tsaron gabar ruwan kasar Italiya sun ce sun tsamo gawarwakin ‘yan ci-rani biyar a tekun Bahrum, bayan sun ceto wasu kimanin 300 da ran su. Jami’an sun ce kwale kwalen ‘Yan ci-ranin ya nutise ne a teku.

Daruruwan 'Yan ci-rani ke mutu a teku a kokarin tsallakawa zuwa Turai
Daruruwan 'Yan ci-rani ke mutu a teku a kokarin tsallakawa zuwa Turai REUTERS
Talla

‘Yan ci ranin na cikin kwale kwalen marar inganci guda biyu, da kuma wasu na kamun kifi guda 3.

Akalla bakin da ke neman ingancin rayuwa 145,000 suka isa Italiya a cikin wannan shekara.

Sannan Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla ‘Yan ci-rani da yan gudun hijira 3,626 suka mutu a kokarin tsallakawa zuwa Turai a tekun Bahrum.

Batun kwararar 'Yan gudun Hijira da 'yan ci-rani na cikin manyan batutuwan da za su mamaye taron shugabannin kasashen Turai a yau Alhamis.

Kungiyar Tarayyar ta yi barazanar katse bayar da tallafi ga kasashen Afrika da suka ki ba ta hadin kai wajen karbar 'yan gudun hijirar da ta koro.

Wannan matakin dai zai fara aiki ne kan ‘yan gudun hijirar Najeriya da Nijar da Senegal da Habasha da kuma Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.