Isa ga babban shafi
Libya

‘Yan ci rani 84 sun bata a tekun Libya

Masu aikin ceto na ci gaba da neman ‘Yan ci-rani kimanin 84 da suka bata a tekun Libya bayan kifewar kwale-kwalen da suke ciki a ranar Juma’a. Rahotanni sun ce wani babban jirgin ruwan Italiya ya yi nasarar ceto rayuwar wasu 26 daga cikin wadanda kwale kwalen ya kife da su a teku.

Jami'an Italiya sun ceto 'Yan ci rani da dama a tekun Lampedusa
Jami'an Italiya sun ceto 'Yan ci rani da dama a tekun Lampedusa REUTERS
Talla

Yanzu haka kuma Jami'an agaji da Sojojin ruwan Italiya na ci gaba da aikin lalaben sauran mutanen da suka nutse a teku kusa da Lampedusa.

Hukumomin Italia na kokarin tantance kasashen ‘Yan ci-ranin da aka yi nasarar tsamowa daga teku.

Sama da mutane 350,000 suka tsallaka zuwa Italiya ta kwale kwale daga Libya tun a 2014, yawancinsu masu kauracewa yake yake da kuncin talauci a kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.