Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ba za ta canza matsayi ba akan ‘Yan ci-rani

Shugaba Francois Hollande na Faransa, ya ce ficewar Birtaniya daga kungiyar Turai, ba zai sa Faransa ta canza matsayinta a game da yarjejeniyar hana kwararar baki ‘yan ci-rani da ke tsakanin Faransa da Birtaniya ba.

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Francois Hollande da ke Magana a karshen taron kwanaki biyu da shugabannin kasashen yankin Turai 27 suka gudanar a birnin Brussels na kasar Belgium, ya ce yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Faransa da Birtaniya domin hana kwararar baki ta mashigin Calais, tana nan daram.

Hollande ya ce waccan yarjejeniya da kasashen biyu suka kulla, ba ta da nasaba da dalilan ficewar Birtaniya daga gungun Turai, kuma ya zama wajibi ga Faransa ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar.

Tun a shekara ta 2003 ne kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar, wadda kuma lokaci zuwa lokaci shugabannin kan zauna domin sake jaddadawa lura da yadda ake samun kwarar baki a yankin Turai baki dayansa.

Kimanin watanni uku da suka gabata jami’an tsaron Faransa sun yi amfani da karfi domin kwashe wasu baki sama da dubu hudu da suka yi cincinrindo a kusa da mashigin Calais suna kokarin shiga Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.