Isa ga babban shafi
Faransa

Muhawarar Jam'iyyar Republican na Faransa kan zaben 2017

Masu neman shugabancin Faransa a Jam’iyyar Republican mai adawa za su gudanar da wata babbar muhawara a yau Alhamis domin tsayar da daya daga cikinsu a matsayin dan takarar Jam’iyyar a zaben da za a gudanar a 2017.

'Yan takarar Jam’iyyar Republican a zaben Faransa na shekarar 2017
'Yan takarar Jam’iyyar Republican a zaben Faransa na shekarar 2017 Joël SAGET Kenzo TRIBOUILLARD Martin BUREAU Lionel BONAVENTURE /
Talla

‘Yan takarar sun hada da tsohon shugaban kasa Nicolas Sarkozy da tsohon Firaminista Alain Juppe da sauran ‘Yan takara 5 da suka hada da Francois Fillon tsohon minister a gwamnatin Jacques Chirac.

Gwamnatin Francois Hollande, wanda ke fuskantar kalubali musamman a fanin tsaro, har yanzu bai bayyanan matsayinsa na sake tsayawa takarar ba.

Sai dai ga dukkan alamu jam’iyyar Hollande ta Socialist na fuskantar koma baya a kuri’un jin ra’ayin ‘yan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.