Isa ga babban shafi
EU-Birtaniya

Birtaniya na fargaban kafa rundunar EU

Kasar Birtaniya ta lashi takobin nuna adawa da shirin kungiyar Tarayyar Turai na kafa wata rundunar tsaro ta musamman, abin da ta ke ganin zai rage wa kungiyar tsaro ta NATO karsashi.

Ministan tsaron Birtaniya Michael Fallon
Ministan tsaron Birtaniya Michael Fallon REUTERS/Hadi Mizban/Pool
Talla

Shirin kafa sabuwar rundunar na zuwa ne bayan Birtaniya ta zabi ficewa daga kasashen Turai a kuri’ar raba gardamar da ta kada a cikin wannan shekarar.

A yayin da Birtaniya ta lashi takobin kalubakntar wannan shirin da ba za ta ci gaciyarsa ba, shugaban kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya bayyana cewa, matakin ba zai gurgunta huldar kasashen da ke kunshe a cikin NATO ba kamar yadda Birtaniya ke zato.

Takardar dai na zuwa ne a yayin da ministocin kasashen na Turai suka gana a birnin Bratislava na Slovakia don tattaunawa kan hanyoyin bunkasa sha’anin tsaro a tsakanin kasashensu.

Kuma da ma wannan matakin na daga cikin muhimman batutuwan da shugabannin Turai suka mayar da hankali a kai a wani taron da suka gudanar ba tare da Birtaniya ba a farkon wannan watan.

Ministan tsaron Birtaniya, Micheal Fallon da ya halarci taron na yau ya ce, dole ne kungiyar tsaro ta NATO ta ci gaba da zama ginshiken tsaro a Birtaniya da sauran kasashen Turai, amma ba wannan sabuwar runduna ba.

Mr. Fallon ya kara da cewa, za su ci gaba da adawa da shirin kafa rundunar ta EU wadda za ta tauye karsashin da NATO ke da shi.

A halin yanzu dai kasashe 28 ne ke cikin NATO da suka hada da Birtaniya, amma 22 daga cikin su a Turai suke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.