Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Batun ficewar Birtaniya ya damu Tarayyar Turai

Shugabannin manyan kasashen Turai guda uku da suka hada da Faransa da Jamus da kuma Italiya na shirin gudanar da taro na musamman game da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

Merkel ta Jamus da Renzi na Italiya da Hollande na Faransa na tattaunawa batun ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai
Merkel ta Jamus da Renzi na Italiya da Hollande na Faransa na tattaunawa batun ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai
Talla

Taron matashiya ne ga babban taron Tarayyar Turai da za a gudanar a Bratislava inda za a tantance makomar Birtaniya.

Firaministan Italiya Matteo Renzi wanda ya kira taron tsakanin shi da shugaban Faransa Francios Hollande da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ya ce ya zama wajibi Tarayyar Turai ta farga musamman ga matakin ficewar Birtaniya daga kungiyar.

A sakon da ya wallafa a Facebook Firaministan ya bayyana dalilin kiran taron inda ya ce idan kida ya canza rawa ma za ta canza.

Ganawar shugabannin dai za ta kunshi tattauna batutuwa da suka shafi barazanar hare haren ta’addanci da batun bakin haure da ‘yan gudun hijira da rikicin Syria da dangantakar Turai da Rasha da kuma Turkiya, batutuwan da suka assasa matakin ballewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai.

Shugabannin dai na neman cimma matsaya guda kafin babban taron Tarayyar Turai da za a gudanar a Bratislava domin tantance makomar kungiyar mai mambobi 27.

Ficewar Birtaniya dai daga Tarayyar Turai ya kasance babban kalubalen shugabannin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.