May ta nada sabbin ministocin Birtaniya
Sabuwar Firaminsitar Birtaniya Theresa May ta nada Boris Johnson a matsayin ministan harkokin wajen kasar bayan ta kama aiki a jiya Laraba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mr. Johnson ya kasance jigo wajen ganin al’ummar Birtaniya sun kada kuri’ar ficewa daga kungiyar tarayyar Turai a zaben raba gardamar da suka kada a cikin watan jiya.
Mr. Johnson wanda tsohon magajin garin London ne, ya maye gurbin Philips Hammond wanda ya rike mukamin ministan harkokin waje a gwamnatin David Cameron.
To sai dai shi ma Hammond za a dama da shi a sabuwar gwamnatin, inda a yanzu May ta nada shi ministan kudi sakamakon goyon bayan da ya nuna mata.
Har ila yau, an nada Amber Rudd a matsayin ministan harkokin cikin gidan Birtaniya yayin da aka bar Michael Fallon akan mukaminsa na ministan tsaro.
Kazalika, Misis May ta nada David Davis a matsayin ministan da zai kula da shirin ficewar Birtaniya daga tarayyar turai kuma a karon farko kenan da aka kirkiri wannan kujerar a Birtaniya.
Ana saran nan gaba kadan za ta nada ministocin lafiya da ilimi da kuma ayyuka da harkokin kasuwanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu