Masarautar Birtaniya na ziyara a Faransa
Yau ake saran 'ya'yan gidan sarautar Birtaniya za su ziyarci Faransa domin halartar bikin cika shekaru 100 da kazamin fadan da aka gwabza a yakin duniya na farko da ake kira "Battle of the Somme".
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yarima William da matarsa Kate da dan uwansa Harry za su halarci filin da aka kashe sojojin Birtaniya da Faransa da kuma Jamus kusan miliyan guda a yakin da aka kwashe watanni 5 ana fafatawa.
Sojojin Birtaniya dubu 20 aka kashe a ranar farko na fara yakin, yayin da aka raunana wasu dubbai.
Wannan shi ne karo na farko da Birtaniya da Faransa za su gudanar da bikin tare, kuma Firaminista David Cameron mai barin gado ya ce zai samu halarta tare da Francois Hollande, shuganam Faransa
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu