Isa ga babban shafi
EU

Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai Sun Faran Taron Ban kwana Da Britaniya

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ko a yanzu a shirye ta ke ta soma tattaunawa da Birtaniya kan ficewar kasar daga kungiyar. 

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai  Donald Tusk
Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Donald Tusk REUTERS/Francois
Talla

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai ne Donald Tusk ya fadi haka a babban taron shugabannin kasashen kungiyar wanda batun ficewar Birtaniya ya mamaye.

Ya ce Turai a shirye ta ke ta soma bin hanyoyin rabuwa da Birtaniya tun ma a yau, ba tare da wata nadama ba.

A cewarsa 'Za mu bi matakan da suka dace domin a shirye muke'.

Ya kara da cewa 'Amma ina son in jaddada cewa ba za'a fara bin matakan ficewar Birtaniya ba sai an duba wasu bukatu na dangantaka

Ya ce 'Daga ranar ficewar Birtaniya na ji ne kamar wani na kud da kud dani ya fice ya bar gidanmu da kuma jin irin illar da hakan zai haifar'.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.