Rasha-Ukraine
Rasha ta saki direbar jirgin saman Ukraine
Hukumomi a Rasha sun saki direbar jirgin sojin saman Ukraine bayan ta share tsawon shekaru biyu tsare a gidan yarin kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
A yau laraba ne Nadiya Savchenko mai shekaru 35 a duniya ta isa kasar ta Ukraine, inda ake kyautata zaton shugaban kasar Petro Poroshenko zai ba ta wata lambar girmamawa.
Da farko dai kasar ta Ukraine ce ta fara sallamar wasu sojojin Rasha biyu Aleksandr Aleksandrov da Yevgeny Yerofeyev wadanda aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari saboda samun su da taimakawa ‘yan aware da ke neman ballewa daga kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu