Isa ga babban shafi
Austria

Alexander Van der Bellen ya lashe zaben Austria

Alexander Van der Bellen na jam’iyyar masu ra’ayin karre muhalli shi ya yi nasarar lashe zaben shugabancin kasar Austria da kashi 50.3 cikin 100

Alexander Van der Bellen sabon shugaban kasar Austria.
Alexander Van der Bellen sabon shugaban kasar Austria. Reuters/路透社
Talla

'Yan takarar 2 da suka kara a zagaye na 2 na zaben shugabancin kasar sun hada da Norbert Hofer da kuma Alexander Van der Bellen, sun dai zo kafada da kafada ta fannin yawan kuri’u da farko kafin daga bisani sakamakon kiddayar na yau litinin ya tabbatar da Bellen a matsayin wanda ya yi nasara.

Yanzu haka dai hankulan jama’a a kasar da ma sauran kasashen yankin Turai sun karkata ne zuwa ga kasar domin sanin yadda Bellen zai jagoranci kafa gwamnati bayan nasarar da ya samu akan Hofer mai ra’ayin rikau.

Alkalumman da aka fitar zuwa yammacin jiya na nuni da cewa mutanen biyu na gogayya ne da juna ta fannin kuri’u, duk da cewa da farko an yi hasashen dan takarar na masu ra’ayin rikau, wanda kuma sau da dama yana fitowa fili domin nuna kyamar baki ne zai yi nasara ba tare da wata matsala ba.

A zagayen farko na zaben da aka gudanar ranar 24 ga watan afrilun da ya gabata, karo na farko a tarihi wadannan jam’iyyun biyu sun yi nasarar zuwa zagaye na biyu a cikin shekaru sama da 60, yanzu dai an zura ido don ganin yadda Bellen zai gudanar da mulkin kasar bayan wannan zaben da ya matukar janyo hankulan al'umma ciki da wajen kasar ta Austria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.