An farfado da tattaunawar sulhu da ‘yan Taliban
Pakistan na daukar nauyin wani taro domin farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin ‘yan Taliban da kuma gwamnatin Afghanistan
Wallafawa ranar:
Akwai wakilan kasashen Amurka, China, Pakistan, Afghanistan da kuma Taliban da ke halartar wannan taro, a kokarin da ake na ganin cewa ‘yan kungiyar ta Taliban sun sulhunta da gwamnatin Kabul.
A makon da ya gabata gwamnatin kasar ta Afghanistan ta rataye wasu 'ya'yan kungiyar Taliban guda 6, wanda shi ne irin sa na farko tun bayan mulkin shugaba Hamed Karzai.
Taliban dai ta dage da a janye dakarun kasashen waje sama da 13,000 daga Afghanistan kafin ta amince da batun sulhu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu