Isa ga babban shafi
Pakistan

Taliban ta dauki alhakin harin Pakistan

Wani reshe na kungiyar Taliban da ake kira Jama’atul Ahrar ya dauki alhakin kai kazamin harin da ya hallaka mutane sama da 72 a Lahore na kasar Pakistan.

Daya daga cikin wadanda harin Lahore ya ritsa da su.
Daya daga cikin wadanda harin Lahore ya ritsa da su. ARIF ALI / AFP
Talla

Mai magana da yawun kungiyar, ya bayyana ta kafar intanet cewa, sun kai harin ne kan Kiristocin da ke bikin Easter.

Shaidun gani da ido sun ce, an kai harin ne a dandalin da ke dauke da daruruwan mutane inda nan take aka kashe 65 yayin da kusan 340 suka samu raunuka.

Firaminsitan Pakistan Nawas Sharif ya bayyana kaduwarsa da harin, yayin da takwaransa na India Narendra Modi ya aike da sakon ta’aziya inda ya ce su na tare da mutanen kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.