Isa ga babban shafi
Amurka

Zaben fidda gwani a jihohi 12 na Amurka

A yau talata ne wadanda ke neman tsayawa takaran shugabancin Amurka zasu fafata a Jihohi 12 da ake kira Super Tuesday, wanda ke da matukar tasiri a zaben fidda gwanin shugaban kasa.

Bernie Sanders da Hillary Clinton 'yan takara a inuwar  jam'iyar Democrats
Bernie Sanders da Hillary Clinton 'yan takara a inuwar jam'iyar Democrats REUTERS/Mike Segar
Talla

Zaben na yau shine zai nuna wanda manyan Jam’iyun kasar zasu sa a gaba a matsayin dan takara dan samun wanda zai maye gurbin shugaba Barack Obama a zaben gama garin da za’ayi a watan Nuwamba.

Hillary Clinton ce a sahun gaba karkashin inuwar jam’iyar Democrat a yayin da attajiri Donald Trump ke da yawan tazara a tsakaninsa da sauran abokan takara na jam’iyar Republican.

Sauran ‘yan takaran sun hada da Bernie Sanders na Jam’iyar Democrat sai kuma Senator Ted Cruz da Marco Rubio da kuma Ben Carson duk a jam’iyar Republican

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.