Majalisar Faransa na muhawara kan kundin tsarin mulki
‘Yan majalisar kasar Faransa sun fara tafka mahawara a yau jumma'a akan bukatar nan ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara a fannin tsaro.
Wallafawa ranar:
Hakan na nufin Faransa za ta iya janye fasfo tare da tasa keyar mutum zuwa kasarsa ta asali muddun aka same sa da laifin aikata ayyukan ta’addanci
Bukatar yin gyarar dai ta biyo bayan munanan hare-haren ta’addancin da aka kai a birnin Paris a bara da suka hallaka mutane sama da 100, inda bincike ya nuna cewa ' yan ta’addan 'yan asalin kasashen ketare ne da ke da takardun zama a Faransa.
Faransa dai na ci gaba da karfafa matakan tsaro a ciki da wajen kasar don kare al’ummarta daga hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu