Isa ga babban shafi
Birtaniya

‘Yan Majalisar Birtaniya sun yi muhawara kan Trump

Majalisar Birtaniya ta fara muhawara game da matakin haramtawa Dan takaran shugabancin Amurka a Jam’iyar Republican Donald Trump shiga kasar saboda abin da ta kira munanan kalaman da ya ke yi akan al’ummar Musulmi.

Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican
Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Mahawarar ta biyo bayan sanya hannu kan takardar koke da mutane sama 575,000 suka yi inda suka bukaci haramta wa Trump shiga kasar baki daya.

Jack Dromey, Dan Majalisa daga Jam’iyyar Labour ya bayyana Trump a matsayin wawa, wanda ya ke da damar nuna wawancinsa, amma kuma ba shi da hurumin yin haka a kasarsu.

Sai dai wasu da dama daga cikin ‘Yan Majalisun ba su amince da matakin haramta wa Trump shiga Birtaniya ba, a cewarsu ana iya kawar da tunanin shi ta hanyar muhawara.

Tuni dai gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa ba zata haramtawa Trump shiga kasar ba, kuma har yanzu majalisar kasar ba ta kada kuri’ar amincewa da matakin ba.

Donald Trump dai na takarar shugabancin Amurka ne a karkashin jam’iyyar Republican. Amma kalamansa kan haramtawa musulmi shiga Amurka sun janyo suka daga sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.