Isa ga babban shafi
Jamus

AFP ya zabi Merkel matsayin gwarzon Shekara

Kamfanin Dillancin labaran Faransa ya bayyana shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a matsayin gwarzon shekarar bana saboda rawar da ta taka a shekarar 2015 mai karewa.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Daukacin ma’aikatan kamfanin suka kada kuri’ar amincewa da Merkel saboda rawar da ta taka wajen matsalar bakin da ke kwarara nahiyar Turai da kuma matsalar bashin kasar Girka.

Nahiyar Turai dai ta fuskanci babban kalubale na karbar baki ‘Yan gudun hijira da ke gujewa rikici a kasashen Syria da Iraqi. Kuma Kasar Jamus karkashin jagorancin Angela Merkel ta ce zata karbi ‘Yan gudun hijira Miliyan guda.

Shugaban kasar Russia Vladimir Putin da ya lashe kyautar bara shi ne ya zo na biyu kan yadda ya sauya alkiblar rikicin Syria duk da yadda kasashen Yammacin duniya suka juya masa baya.

Akwai kuma Fafaroma Francis da aka karrama kan rawar da ya taka na sasanta kasashen Amurka da Cuba da suka shafe sama da shekaru 50 suna gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.