Isa ga babban shafi
Forbes

Mata : Merkel ce mai karfin fada aji a duniya

Mujallar Forbes a Amurka ta bayyana shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a matsayin mai karfin fada aji kuma tauraruwa da ke jagorantar matan duniya musamman wadanda ke taka rawa a fagen siyasa.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel REUTERS/Yves Herman
Talla

Wannan ne karo na biyar jere da juna da Merkel ke samun wannan matsayi a gaban tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da ke a matsayi na biyu.

Matar Attajirn duniya Melinda Gates ita ce aka bayyana a matsayi na uku.

Shugabar asusun lamuni Christine Lagarde ce a matsayi na shida sai shugabar Brazil Dilma Rousseff a matsayi na bakwai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.