Isa ga babban shafi
EU

EU na shirin gudanar da taro kan tunkarar ta'addanci a kasashen su

Ministocin cikin gidan kasashen Turai da na shari'a za su gudanar da wata tattaunawa a ranar Juma’a mai zuwa kan barazanar tsaro da suke fuskanta domin duba hanyar tunkara matslar, bayan harin Ta’addacni da aka kaiwa birnin Paris tare da kashe mutane 129.

REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Taron tattaunawa da za a gudanar a birnin Brussels, a cewar Ministan tsaron cikin gidan Luxembourg Etienne Schneider ya zama wajibi Turai su hada kai wajen tunkarar ta’addanci kafin abin ya wuce tunani.

A wani bangaren kuma Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Jean Claude Juncker ya kare shirin karban bakin haure a Turai inda ya ke cewa mutanen da suka kai hari a birnin Paris ba ‘yan gudun hijira ba ne, batun da ke zuwa bayan wasu kasahen turai sun fara nuna bukatar sauke shirin

Yayin da Hukumomi a Faransa suka bayyana daya daga cikin maharan da cewa dan kasar Syria ne wanda ya shiga cikin turai ta kasar Girka makonni shida baya.

A halin da ake ciki yanzu haka Poland da Slovakia sun ce ba za su aiwatar da yarjejeniyar tarayyar turai na tsugunar da ‘yan gudun hijira wadanda suka fito daga Afirka da gabas ta tsakiya ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.