Isa ga babban shafi
Faransa-Girka

Faransa za ta ci gaba da mu'amula da kasar Girka

Shugaban Faransa Francois Hollande dake rangadi a kasar Girka zai gabatarwa wakilan majalisar Girka jawabi a yau, inda ake sa ran zai yabawa kasar saboda cigaba da zama cikin kungiyar Turai duk da wahalolin da kasar ta samu kan ta yayinda ake tafka muhawara da kungiyar Turai da Asusun bada lamuni, gameda halin tattalin arzikin kasar.Shugaba Francois Hollande zai kasance shugaban Faransa na uku da yayiwa Majalisar Girka jawabi, bayaga Janar Charles de Gaulle a shekara ta 1953 da kuma Nicholas Sarkozy a 2008. 

Shugaban  Faransa Francois Hollande tareda Shugaban Girka da Firaministan kasar Tspiras
Shugaban Faransa Francois Hollande tareda Shugaban Girka da Firaministan kasar Tspiras REUTERS/Michalis Karagiannis
Talla

Hollande wanda ke tare da rakiyar wasu manyan jami’an gwamnatinsa, ya ce ya ziyarci kasar ne domin karfafawa gwamnatin Alexis Tsipras gwiwa, da muhimman matakai domin kawo karshen rikicin.

Ziyarar Shugaba Hollande na da nasaba da irin kokarin da Faransa da wasu kasashen duniya suka yi a watannin baya domin ceto tattalin arzikin Girka, tareda yi ruwa da tsaki wajen ganin cewa Girka ta ci gaba da kasancewa a cikin gumgun masu amfani da takardar kudin Euro.

Abinda Hollande ya ce wani alhaki ne da ya rataya a wuyansu domin tabbatar da cewa yankin Euro ya ci gaba da kasancewa a dunkule.

Gwmanatin Firaminista Tsipras ta dauki matakai da dama masu muhimmanci saboda haka Hollande ya ce za su yi amfani da wannan dama domin kara jinjina masa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.