Isa ga babban shafi
Girka

Jam'iyyar Syriza ta lashe zaben Girka

Tsohon Firaministan Girka Alexi Tsipiras ya bayyana farin cikinsa da nasarar da Jam’iyar sa ta Syriza ta samu a zaben kasar wanda ya bayyana a matsayin nasarar al’ummar kasar baki da ya. 

lokacin da  Alexis Tsipras ke bayyana farin cikinsa a gaban 'ya'yan Jam'iyyar Syriza a babban birnin Athens.
lokacin da Alexis Tsipras ke bayyana farin cikinsa a gaban 'ya'yan Jam'iyyar Syriza a babban birnin Athens. REUTERS/Alkis Konstantinidis
Talla

Sakamakon zaben da aka gabatar ya nuna cewa jam’iyar Syriza ta Alexi Tsipiras ta  samu gagarumin rinjaye a majalisar kasar da kujeru 145 daga 300 da ake da su, yayin da wasu kananan jam’iyyun da ke ikrarin kishin kasa suka bayyana aniyar su na hada kai da shi.

Yayin da ya ke jawabi a taron jam’iyarsa kan nasarar da suka samu, Tsipiras wanda shine Firaminista mafi Karancin shekaru cikin shekaru 150 da aka yi ana mulkin kasar, ya ce Jam’iyyar Syriza ba za ta mutu ba.

Tsipiras ya bayyana cewar watannin da ke zuwa nan gaba suna da sarkakiya, yayin da yake shirin aiwatar da sauye sauye a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.