Shugaba Francois Hollande na ziyarar aiki a Maroko
A yau asabar shugaban Fransa Francois Hollande zai fara ziyarar aiki a birnin Tanger na kasar Maroko, domin karba gayyatar sarkin kasar Mohammed na shida.
Wallafawa ranar:
Majiyoyin diflomasiyya sun bayyana cewa batun tattalin arziki da kuma sauyin yanayi, na daga cikin muhimman batutuwan da shugabannin kasashen biyu za su mayar da hankali a lokacin wannan ziyara.
Har ila yau ziyarar za ta kasance wata dama ga kasashen biyu domin warware sabanin da suka sama a shekarar bara, bayan da wani alkalin Faransa ya bukaci shugaban hukumar leken asirin Maroko ya gurfana a gabansa bisa zargin cin zarafin bil’adama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu