Isa ga babban shafi
Turkey-Syria-Iraqi

Jiragen yakin Turkiyya sun ci gaba da kai wa Kurdawa farmaki

Sojojin Turkiyya sun kai munanen hare-hare ta sama a yankin kudancin kasar, sa’o’i kadan bayan da wani harin bam ya kashe dakarun kasar 8 a jiya laraba.

Wasu mayakan PKK a kudancin Turkiyya
Wasu mayakan PKK a kudancin Turkiyya AFP / SAFIN HAMED
Talla

Rahotanni sun ce jiragen yakin kasar sun fadada yankunan da suke kai wa hare-haren zuwa 13 inda mafi yawan mazaunansu Kurdawa ne.

Kungiyar ‘yan tawayen Kurdawa ta PKK ta ce ita ta dasa bam wanda ya tashi a lokacin da ayarin motocin sojin kasar ke wucewa a jiya, lamarin da ya haddasa mutuwar dakarun na gwamnati 8 da kuma raunana wasu da dama.

Gwamnatin Turkiyya dai ta tsananta kai hari akan yankunan Kurdawa a cikin wata daya, a daidai lokacin da kasar ke fuskantar wata barazanar tsaro daga mayakan kungiyar IS da ke ikirarin yin jihadi daga kasashen makotanta Iraki da Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.