Isa ga babban shafi
Turkey-Iraqi

Kurdawan PKK sun umarci 'ya'yan Kungiyar su fice daga Iraqi

Shugabannin kungiyar Kurdawa PKK a Iraqi, sun bukaci ficewar mayakansu daga yankuna kurdawa da ke kasar, domin kare rayukan fararan hula da hare-hare sama da Turkiya ke kaiwa ke hallakawa.

Kurdawa a Iraqi
Kurdawa a Iraqi REUTERS/Azad Lashkari
Talla

A wata sanarwa da suka fitar ofishin shugaban kurdawa yankin Massud Barzani ya ce bai kyautu fararran hula suke rasa rayukansu ba saboda su.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai loakcin da rahotannin ke cewa Sama da mayakan Kurdawa 260 ne suka rasa rayukansu a mako guda na jerin hare-haren da Turkiya Ke kaiwa kan mayakan a arewacin iraqi, yayin da ake samu asaran rayukan fararran hula da dama.

Turkiya dai ta lashi takobin kawar da ayyukan ta'addanci da ke neman zama barazana a  kasarta, lamarin da ya sa kasar daukan matakin kaddamar da hare-haren sama a Iraqi da Syria kan mayakan ISIL da na Kurdawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.