Isa ga babban shafi
Girka

Kungiyar MSF ta damu kan farmakin da ake kaiwa bakin haure

Kungiyar likitoci mara iyaka ta MSF ta bayyana rashin jin dadinta bayan ‘yan ciranin dake kokarin isa tsibirin Kos na Kasar Girka sun yi korafi kan farmakin da ake kai musu a teku.

Jirgin ruwa makare da Bakin haure a Teku
Jirgin ruwa makare da Bakin haure a Teku REUTERS/Guglielmo Mangiapane
Talla

Bakin haure da dama da suka isa tsibirin na Kos daga kasashen Iraki da Syria a makon daya gabata, sun shaidawa kamfanin dillacin labarann Faransa cewa, wasu yan bindiga rufe da fuskokinsu sun kai musu hari a Tekun tare da sace kayayyakinsu da ya hada da man Fetur harma da Motoci.

A ranar daya ga watan nan na Agustan ne, masu tsaron gabar ruwan Girka suka ce, sun cafke mutane uku a tsibirin samos dake farautan bakin haure dake kokarin shiga kasar daga Turkiyya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.