Isa ga babban shafi
Ukraine

EU ta la’anci harin da aka kai wa tawagar masu sa ido a Ukraine

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta yi allawadai da harin da aka kai wa motocin sulken jami’an sa ido, da ke kula da yarjejeniyar zaman lafiya a yankunan da ke hannun ‘yan tawaye a gabashin kasar Ukraine.

Motocin da aka lalata na Hukumar sa ido ta Turai OSCE a Ukraine
Motocin da aka lalata na Hukumar sa ido ta Turai OSCE a Ukraine Reuters/路透社
Talla

Kungiyar ta kuma bukaci dukkan bangarorin da ke rikici da juna su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya.

Tawagar, masu sa ido daga Kungiyar Tsaro da Hadin gwiwan kasashen Turai ta OSCE, sun bayyana cewa an lalata musu motoci hudu a Otel dinsu.

Sanarwar da kungiyar ta EU ta fitar tace ba za ta amince da kone motocin na tawagar ta OSCE, da aka yi a birnin Donetsk ba, lamarin da ta bayyana da cewa abin takaici ne.
Kungiyar ta bayyana cewa tawagar ta musamman, ta taka rawar da ke da muhimmanci, wajen sa ido da tabbatar da yarjejeniyar birnin Minsk, da ita ce kashin bayan kokarin samar da zaman lafiya a Ukraine.

Kungiyar ta OSCE, tace da gangan aka cinna wa 4 daga cikin motocinsu wuta.

Don haka ne ta bayyana matakin a matsayin wani yunkurin dawo da hannun agogo baya a game da sa ido da ta ke yi, sai dai kuma kungiyar tace ba gudu ba ja da baya a wannan aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.