Isa ga babban shafi
Britaniya

Wani dan Majalisar Britaniya ya yi murabus bayan aikata asha

Wani dan majalisar masarautar Britaniya ya ajiye mukaminsa, bayan da wasu bayanai suka ce yayi mu’amala da karuwai, da amfani da miyagun kwayoyi.

Dan Majalisa John Sewel
Dan Majalisa John Sewel DR Aberdeen University
Talla

Jaridar Sun da ake bugawa a kasar ta Britaniya mallakin Rupert Murdoch ce ta bankado labarin inda ta bugo hoton Lord John Sewel, yana shakar hodar Iblis daga kan nono wata karuwa.

Wannan yasa aka sake ci gaba da kiraye kirayen neman a duba yadda ake daukar ma’aikatan majalisar, bangaren wadanda ba zabensu ake yi ba.

Sewel, mai shekaru 69, ya nemi afuwar jama’a, saboda bakin ciki da abin kunyan da ya aikata.
A yau talata ne dai dan Majalisar masarautar Britaniyan ya yi murabus daga mukaminsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.