Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya za ta yi zaben raba gardama kan EU

Gwamantin David Cameron Firaministan Birtaniya ta bayyana cewa zata kada kuri’ar raba gardama dangane da batun ficewar kasar daga Kungiyar Turai masu amfani da takardar kudin yuro. Sarauniya Elizabeth ta biyu ce ta bayyana haka a wani jawabi da ta gabatar a majalisar dokokin Kasar.

Sarauniyar Elizabeth
Sarauniyar Elizabeth Reuters
Talla

A cikin jawabin, Sarauni Elizabeth tace Birtaniya za ta fuskanci tsauraren matakan rage kashe kudade.

A lokacin da ta ke bada jawabai dangane da tsare tsaren sabuwar gwamnati a shekarar farko, sarauniya Elizabeth mai shekaru 89 da haihuwa ta tabbatar cewa kasar Birtaniya zata fuskanci tsauraran matakai domin rage yawan kudaden da ta ke kashewa.

Wannan zai shafi tsare tsaren da aka fitar domin tallafawa masu matsakaicin samun kudi ‘yan asalin Birtaniya dangane da bai wa kananan yara ilimi kyauta da ma bangaren kula da lafiyar al’umma, inda ake kashe makudan kudade.

Gwamanatin Birtaniyar ta yi alkawarin ba za ta kara yawan kudin haraji ba a manyan bangarori uku har nan da shekaru biyar masu zuwa.

A cewar Firaministan Kasar David Cameroon, jawabin Sarauniyar na da tasiri ga ilahirin ‘yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.