Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande na cikin hatsari kan yadda ake tsaronsa

Wasu mutane na kusa da shugaban Faransa Francois Hollande, sun ce shugaban na a cikin hatsari saboda akwai rauni matuka a game da yadda ake bai wa shugban kariya ta tsaro. Sai dai wasu na ganin shugaban ne ke bukatar yin walwala don tafiyar da sha ‘anin rayuwarsa.

Shugaban Faransa François Hollande
Shugaban Faransa François Hollande REUTERS/Enrique de la Osa
Talla

A wata zantawa a asirce da jaridar Le Monde da ake bugawa a kasar, mutanen wadanda ke aiki da runduna ta musamman da ke kare shuugaban ta GSPR, sun ce lura da irin halin da duniya ke ciki na karuwar ayyukan ta’addanci, akwai bukatar kare daukar sabbin matakai domin kare Francois Hollande.

Wani lokaci a can baya an taba bayar da labarin cewa, Hollande a matsayinsa na shugaban kasa, yana zuwa wajen wata farkarsa shi kadai, kuma wani karon ma akan Babur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.