Isa ga babban shafi
Birtaniya

Ana babban Zabe a Birtaniya

Jama’ar Birtaniya na kada Kuri’a domin zaben ‘yan majalisun kasar wanda ake hasashen cewar babu wata jam’iyya da za ta iya samun nasara kai tsaye don kafa gwamnati. Rahotanni sun ce a karon farko tun shekarar 1974 wannan ne karon farko da za a samu gwamnati marar rinjaye.

Jami'an zaben Birtaniya a wata mazaba da ke Doncaster arewacin Ingila
Jami'an zaben Birtaniya a wata mazaba da ke Doncaster arewacin Ingila REUTERS/Darren Staples
Talla

Da misalin karfe 6 na safe agogon GMT aka bude runfunar zabe, kuma al’ummar kasar za su ci gaba da kada kuri’a har zuwa 10 na dare.

Ana sa ran samun sakamakon zaben zuwa gobe Juma’a.

Al’ummar Birtaniya za su zabi ‘Yan majalisu daga Jam’iyyar Firaminista David Cameron da Jam’iyyar Labour ta ED Maliband da kuma wasu kananan Jam’iyyun siyasa da ke fafatawa a zaben kasar.

Jam’iyyu 7 ke neman goyan bayan jama’a don samu nasara a zaben da ake ganin babu wata jam’iyyar da za ta samu gagarumin rinjaye.

Firaminista mai ci David Cameron na jam’iyyar Conservative na fuskantar suka kan yadda gwamnatin sa ke tinkarar matsalar baki da kara yawan haraji ga al’ummar kasar da kuma kalubalantar kungiyar kasashen Turai.

Babban mai adawa da shi Ed Miliband, jagoran jam’iyyar Labour, na ci gaba da samun tagomashi, sai dai har yanzu akwai mutanen da ba su yafewa gwamnatin su ta baya ba kan yadda ta jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki.

Nick Clegg da ke jagoranci Liberal Democrat, kuma mataimakin Firaminista, na fuskantar kalubale saboda yadda suka kasa bayar da gudumawar kirki a cikin gwamnati mai ci, abin da ake ganin zai sa jam’iyyarsu ta rasa kujeru da dama a majalisar kasar.

Sauran 'Yan takaran sun hada da Nigel Farage na UK Independence Party da Nicola Sturgeon na Scottish National Party da Lean Wood na Plaid Cymru da Natalie Bennett na Green Party.

Masu sharhi kan siyasar kasar na kallon fafatawar tsakanin Conservative da Labour, sai dai sun ce da wuya a samu jam’iyya guda da za ta samu nasarar kafa gwamnati ita kadai.

Sakamakon zaben dai na iya sanya Birtaniya cikin yanayin ficewa daga kungiyar kasashen Turai da kuma yiyuwar ballewar Yankin Scotland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.