Isa ga babban shafi
Brazil

Shugabar Brazil na shirin yaki da cin hanci

Shugabar Kasar Brazil, Dilma Rousseff, ta sanar da shirinta na yaki da cin hanci, bayan badakalar cin hanci da ta dabaibaye jiga jigan jam’iyyarta a yanzu

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff
Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Rousseff ta sanar da shirin nata ne, bayan badakalar cin hancin a ma’aikatar man Kasar, na Petrobras da kuma ake zargin wasu jiga jikan jam’iyyarta a kai.

Rousseff ta bayyana cewa, gwamnatinta ba zata amince da cin hancin da rashawa ba, yayinda ta jaddada kudirin gwamnatin na hukunta masu karen tsaye ga doka

Yanzu dai, shirin zai kunshi kwace kadarorin 'yan siyasa da suka mallaka amma ba suka kasa da bada cikakkun bayanai kan yadda suka same su

A karshen makon daya gabata ne, dubun dubatan yan kasar ta Brazil suka gudanar da zanga zanga a titinan kasar, inda suka soki gwamnatin Rousseff, yayinda a yanzu, akwai kimanin yan siyasa 50 dake fuskantar tuhuma kuma akasarinsu, nada kakkyawar alaka da Rouseff.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.