Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya kalubalanci kassahen Duniya kan Mayakan Siriya

Shugaba Francois Hollande na Faransa, ya ce har yanzu yana nadamar yadda kasashen duniya suka kin yin amfani da karfin soja domin kawo karshen kisan kiyashin da ke faruwa a Syria, kamar dai yadda ya bayar da shawara a shekara ta 2013

Le président de la République a rendu hommage ce mardi matin dans la cour de la Préfecture de police de Paris aux trois policiers tués la semaine dernière.
Le président de la République a rendu hommage ce mardi matin dans la cour de la Préfecture de police de Paris aux trois policiers tués la semaine dernière. AFP
Talla

Shugaban Hollande wanda ke gabatar da jawabi a gaban daruruwan sojojin kasar da ke kan hanyarsu ta zuwa Iraki domin fada da ayyukan ta’addanci, ya ce har kullum yana nadamar yadda kasashen duniya suka ki karbar shawararsa, kuma da kasashen duniya sun afka wa Syria, to lalle da an kawo karshen zubar da jini da kuma hana bazuwar ayyukan ta’addanci.

Shugaban na Faransa ya ce kamata ya yi a tura sojojin a karshen watan agusta zuwa farkon watan satumbar shekarar ta 2013, kuma a lokacin Faransa na a cikin shirin domin ba da nata sojojin.

Francois Hollande dai na jawabin ne ga wani ayarin sojoji dauke da makamai da ke cikin makeken jirgin ruwan yakin kasar mai suna Charles de Gualle akan hanyarsa ta zuwa kasar Iraki, inda yanzu haka sojojin kawance ke fada da mayakan da ke da’awar jihadi.

Shugaban na Faransa ya ce kasar shi za ta ci gaba da daukar matakai na fada ta’addanci, lura da yadda yake shafar kasar da kuma sauran kasashen duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.