Isa ga babban shafi
Australia-Faransa

Hollande: Ziyarar Shugaban Faransa ta farko a Australia

Shugaban Faransa Francois Hollande ya zama shugaban kasar Faransa na farko da ya kai ziyara kasar Australia, inda ya ke saran bunkasa huldar tattalin arzikin tsakanin kasashen biyu. Fadar shugaban kasar tace Hollande ya isa Australia ne da tawagar manyan yan kasuwa, kuma ya samu tarbo mai kyau a Sydney.

Firaministan Australia Tony Abbott tare da bakonsa Shugaban Faransa Français François Hollande à Brisbane.
Firaministan Australia Tony Abbott tare da bakonsa Shugaban Faransa Français François Hollande à Brisbane. REUTERS
Talla

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami lokacin da Faransa ta yi gwajin makamin nukiliya a kudancin Pacific a 1990 da kuma batun nutsewar jirgin Faransa a Auckland a 1985, wanda ya haifar da rashin jituwa tsakanin kasashen biyu.

Amma a watan Janairu ne na 2012 Faransa da Australia suka farfado da huldar da ke tsakaninsu, kuma sun yi musayar ra’ayi guda game da rikice-rikecen Afghanistan da Syria da Iran da wasu kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.